A wata sanarwa da ofishin shugaban na Finland Alexander Stubb ya fitar a wannan Laraba, Stubb ya ce yanzu ana ganin wata kungiyar NATO da Turai ke taka muhimmiyar rawa a cikinta.
Sai dai a nashi bangaren, Shugaba Trump ya sake bayyana aniyarsa ta janye Amurka daga kungiyar, inda ya ce yana duba yiwuwar yin jawabi ga ‘yan kasar kan wannan batu.
Trump ya zargi wasu kawayen NATO da kin goyon bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran, yana mai kiran su masu rauni.
Karin bayani: NATO na kara karfi don dakile barazanar Rasha – Merz
Duk da haka, wata doka da aka kafa a shekarar 2023 a lokacin tsohon shugaban kasa Joe Biden na iya zamar ma Donald Trump tarnaki domin zai sha wahla kafin ya iya ficewa
Wannan lamari na nuna yadda ake samun sabani a cikin kungiyar NATO a daidai lokacin da rikice-rikicen duniya ke karuwa.NATO na