Ƙasashen dake cikin ƙungiyar tsaro ta NATO sun ƙi amincewa da buƙatar shugaba Donald Trump na Amurka wajen shiga jerin ƙasashen da za su hana harkokin yau da kullum a tashoshin jiragen ruwan ƙasar Iran.

Wallafawa ranar: 13/04/2026 – 21:03

Minti 2 Lokacin karatu

Trump ya ce za su narkar da duk wani jirgin ruwan Iran da ya matsa kusa da jiragen ruwan Amurka da suka tare duk wata hanyar isa tashoshin, saboda yadda uamarnin ya fara aiki daga yau litinin sakamakon kasa cimma yarjejeniya a ganawar da wakilan Amurka da Iran suka yi a ƙasar Pakistan.

Shugaban na Amurka ya fara bayyana cewar za su yi aikin ne tare da wasu ƙasashen duniya wajen tare jiragen da za su ratsa ta mashigar Hormuz, amma kuma daga bisani sai suka ce matakin na su zai tare jiragen da za su je Iran ne ko kuma waɗanda za su bar ƙasar.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin ƙasashen biyu a ranar 28 ga watan Fabarairu, Iran ce kaɗai ta tare mashigin ruwan Hormuz, ta kuma hana jiragen ruwan ƙasashen duniya motsawa, har sai waɗanda ta bai wa izini.

Wannan mataki ya sanya ƙasar a matsayin guda ɗaya tilo dake iko da mashigin, tare da bayyana shirin karɓar diyya daga jiragen da za wuce ta mashigin.

A jiya Lahadi, shugaba Trump ya sanar da cewar wa’adin da ya bai wa Iran na cewar za su dakile isa tashoshin jiragen ruwan ƙasar zai fara aiki ne daga yau Litinin, amma ƙawayen Amurkar a NATO irin su Birtaniya da Faransa sun fito ƙarara sun ce babu wanda zai sa su shiga yaƙi da Iran, yayin da su ka sanar da wani shiri da su ke yi na tattaunawa a kan yadda za’a buɗe mashigin ruwan Hormuz ɗin.

Ƙin amincewa da buƙatar Trump ya dada fito da irin tsamin dangantakar dake tsakanin su da shugaban na Amurka, wanda ke barazanar janye ƙasarsa daga cikin ƙungiyar tsaron, tare da janye wasu sojojin ƙasar dake Turai saboda yadda suka hana jiragen yaƙin Amurka amfani da sararin samaniyar su wajen kai wa Iran hari.

Firaministan Birtaniya Keir Starmer, yayin jawabi ga majalisar dokokin ƙasar sa a yau Litinin, ya ce basa goyan bayan tare tashoshin jiragen ruwan Iran, kuma babu wanda zai sa su shiga yaƙin da ba na su ba.