Ƙungiyar tsaro ta NATO da wasu manyan shugabannin jam’iyyar Republican a Amurka sun nuna matuƙar damuwa game da matakin da gwamnatin shugaba Donald Trump ta ɗauka na janye sojojin Amurka kusan 5,000 daga Jamus.
Wallafawa ranar: 03/05/2026 – 10:00Chanzawa ranar: 03/05/2026 – 10:00
Minti 1 Lokacin karatu
Wannan mataki ya biyo bayan takun-saƙa tsakanin Amurka da ƙawayenta na Turai, musamman kan batun yaƙin da ake yi da Iran da kuma kalaman Shugaban Jamus, Friedrich Merz.
Shugabannin kwamitocin tsaro na Majalisar Dattijai da na Wakilai, Senator Roger Wicker da Wakilin Mike Rogers, sun fitar da sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka ce matakin zai iya raunata ƙarfin dakile hare-hare kuma yana aika sako mai daɗi ne ga shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Mai magana da yawun ƙungiyar NATO, Allison Hart, ta bayyana cewa ƙungiyar tana aiki tare da Amurka domin fahimtar wannan sabon sauyi na sojojin a Jamus.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Trump ya ɗauki wannan matakin ne a matsayin martani ga ƙin marawa Amurka baya da Jamus ta yi a yaƙinta Iran.
Haka kuma shugaban na Amurka ya yi barazanar ƙara harajin motoci ga ƙasashen Turai zuwa kashi 25.