Gwamnatin Ghana na shirye shiryen ganin an tuso mata ƙeyar ɗan Rashan nan da ake zargi da laifin ɗaukar  bidiyon tsiraicin mata a sirrance, tare da wallafa shi a kafar yanar Gizo, ba tare da izinin su ba.

Wallafawa ranar: 20/02/2026 – 09:04

Minti 1 Lokacin karatu

Matashin da ake zargi da aikata aika aikar, ya bayyana kansa a matsayin ɗan Rasha mai sana’ar waka da kuma wallafe wallafe a yanar gizo.

Mutumin ya ziyarci Ghana ne  inda ya yi afani da kamarar sirri wajen ɗaukar tsiraicin matan da suka yi baɗalar da shi ba tare dasanin su ba, daga bisani ya kuma wallasu a yanar gizo.

Ya yin ganawa da manema labarai, ministan kimiya da fasahar ƙasar, Sam George ya ce tuni suka tun tuɓi jakadar Rasha da ke Ghana don tattaunawa kan lamarin, ganin cewa abinda wanda ake zargin ya aikata, ya saɓawa dokar ƙasar.

Ma’aikatar kula haƙokokin al’umma da wal walan yara ta Ghana, ta ce duk da cewa mutumin ya tsare da ƙasar, amma hakan ba zai hana ya fuskanci hukuncin kan abinda ya aikata ba.

Zuwa yanzu dai, gwamnatin Ghana ta sha alwashin sai taga abin da ya ture wa buzu naɗi kuma idan har aka sameshi da laifi, to zai iya zama gidan waƙafi  na shekara 25, karƙashin dokar ƙasar ta 2020.