Gwamnatin Ghana ta ce, ƴan ƙasar 55 ne suka mutu a yaƙin Rasha da Ukrane, yayin da ake tsare da  2, a wani mataki da ake alaƙantashi da yaudarar matasan Afrika sama da dubu 1,780 da Rasha ta ɗauka a ƙasashe 36 .

Wallafawa ranar: 02/03/2026 – 09:08

Minti 1 Lokacin karatu

Ministan harƙoƙin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, da ke bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya na mai cewa, sun kadɗamar da wani shiri na daƙile tsarin yaudarar ƴan ƙasar domin samun ayyukan yi a ƙasashen waje, ta hanyar rusa haramtattun tsare-tsaren ɗaukar ma’aikata da aka yi wa laƙabi da ‘dark web’.

Babban jami’in diflomasiyar na Ghana, ya ce, duk da kyakkywar alaƙar tattalin arziki da ta diflomasiya da ke tsakanisu da Rasha, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, wajen wayar da kan al’ummarsu game da hanyoyin da ya kamata su bi wajen samun ayyukan yi a ƙetare.

Jami’in ya kuma bada misalin yadda wasu ƴan Afrika Ta Kudu suka gamu da ajalinsu a yaƙin na Rasha da Ukrane kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta bada tabbacin dawowa da wasu gawarwakin wasu daga cikin su .

Ka zalika, rahoton leken asirin Kenya, ya sanar da cewa  ƴan ƙasar sama da dubu guda aka ɗauka aikin yaƙin amma kuma an sami nasarar ceto wasu 27 daga cikin su.

Ablakwa, ya ƙara jaddada cewa, suna da labarin ƴan Ghanan kusan 300 da aka yaudaresu zuwa yaƙin cikin rashin sani, wanda kuma ba yakin su ba ne dan haka ba za’a bar matasan ƙasar kara zube ba,  za’a ci gaba da wayar musu da kai.