Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya tabbatar da cewa aƙalla ‘yan ƙasar Ghana 55 ne suka riga mu gidan gaskiya a yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Wallafawa ranar: 28/02/2026 – 07:48Chanzawa ranar: 28/02/2026 – 07:49

Minti 1 Lokacin karatu

Baya ga mutane 55 da aka kashe, ministan ya bayyana cewa kimanin ‘yan Ghana 272 ne aka yaudara don shiga fagen yaƙin tun daga shekarar 2022.

Akwai wasu ‘yan ƙasar guda biyu da Ukraine take tsare da su a matsayin fursunonin yaƙi bayan an kama su suna taimakawa dakarun Rasha.

Hukumomin Ghana sun bayyana cewa an yaudari matasan ne ta yanar gizo da kuma hanyoyin safarar mutane na ba bisa ƙa’ida ba, inda aka yi musu alkawarin ayyuka masu tsoka, amma daga baya aka tura su fagen daga.

Ministan ya bayyana waɗannan alkaluman ne yayin wata ziyara da ya kai birnin Kyiv na ƙasar Ukraine ranar Juma’a, inda ya gana da takwaransa na Ukraine, Andrii Sybiha.

Ablakwa ya bayyana labarin a matsayin abin takaici da firgitarwa, yana mai jaddada cewa wannan ba yaƙin Ghana ba ne kuma gwamnati za ta yi ƙoƙarin ruguza duk wata hanyar ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne adadi mafi yawa na asarar rayuka da aka tabbatar daga ƙasa guda a Afirka tun bayan ɓallewar yaƙin Rasha da Ukraine.