Ministan harkokin wajen Kenya, Musalia Mudavadi, yace zai ziyarci  Moscow, don tattaunawa kan batun mayaudaran da ke daukar ma’aikata ƴan ƙasar zuwa Rasha sannan a  tura su fagen yaƙi da Ukrane da zummar kawo karshen hakan.

Wallafawa ranar: 16/03/2026 – 09:26

Minti 1 Lokacin karatu

Ministan, ya furta hakan ne  ya yi wata ganawa da manema labarai,  biyo bayan gano asarar rayukan wasu yan kenyan da aka yaudara zuwa Rasha, da sunan aiki amma sai su ka tsinci kansu a fagen daga, dan haka sai yace abu ne da ya kamata a kawo karshensa, duk da cewa zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, jami’an Rasha ba su mayar da martani  ba, a kan lamarin.

Ka zalika, zuwa yanzu an sanar da dawowar ƴan Kenyan aƙalla 200 daga Rashan, waɗanda suka fice ba bisa ƙaida ba.

A cewar wasu bayanan sirin Ukrane, Rasaha ta ɗauki ƴan nahiyar Afrika sama da 1,400 daga kasashen 36 ,dan tallafa mata a yakin da ta ke gwabzawa da Ukrane, ko da yake Moscow ta jima tana karyata batun.

Mudavadi, ya bada tabbacin cewa, an ceto wasu ƴan ƙasar  sama da 30 cikin watanni 2 da suka shuɗe, sai dai kuma ana zargin wasu sama da 600 sun faɗa komar mayaudara, da zummar cewa za’a samar musu aiki mai maiko, a wasu ƙasashen.