Ambaliyar ruwa da kuma zabtarewar ƙasa sun yi sanadin mutuwar mutane 20 a ƙasar Tanzania, dai-dai lokacin da ƙasashen yankin gabashin Afrika ke ci gaba da fuskantar ruwan sama mai ƙarfi.
Wallafawa ranar: 28/03/2026 – 08:23
Minti 1 Lokacin karatu
Bayanai sun nuna cewa ambaliyar ruwan ta fara ne tun daren Laraba a yankin Mbeya, wanda hakan ne ya haddasa zabtarewar ƙasar da kuma iska mai tsananin ƙarfi wadda ta riƙa rusa gidajen jama’a da gine-ginen gwamnati.
Mahukunta a yankin Rungwe sun tabbatar da mutuwar mutanen ciki har da ƙaramin yaro guda ɗaya, yayinda suka yi gargaɗin adadin mamatan kan iya ƙaruwa.
Tuni aka umarci mutanen da ke rayuwa a yankuna masu haɗari da su bar guraren, dai-dai lokacin da masu hasashen yanayi suka tabbatar da cewa ana iya samun ƙaruwar ruwan saman.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da makamancin wannan ibtila’i da ya faru a Kenya ya kashe mutane 88, yayinda unguwanni sama da 20 suka shafe da ruwa.
Ambaliyar ta Kenya ta tsananta ne bayan da ɓallewar wasu manyan koguna da suka tumbatsa sanadin ruwan sama ba ƙaƙƙautawa.
Haka abin ya ke a ƙasar Habasha wadda ita ma ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa ya hallaka mutane sama da 80 a farkon wannan wata.
Wannan matsala dai ta ƙara fitowa da matsalolin rashin shirin tunkarar sauyin yanayi daga waɗannan ƙasashe, abinda ke sake jefa fararen hula cikin mummunan yanayi.