{"id":30213,"date":"2026-03-02T10:08:11","date_gmt":"2026-03-02T10:08:11","guid":{"rendered":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/30213\/"},"modified":"2026-03-02T10:08:11","modified_gmt":"2026-03-02T10:08:11","slug":"ghana-ta-tabbatar-da-mutuwar-%c6%b4an-%c6%99asar-55-yayin-yiwa-rasha-ya%c6%99i-a-ukraine","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/30213\/","title":{"rendered":"Ghana ta tabbatar da mutuwar \u01b4an \u0199asar 55 yayin yiwa Rasha ya\u0199i a Ukraine"},"content":{"rendered":"<p>\n                        Gwamnatin Ghana ta ce, \u01b4an \u0199asar 55 ne suka mutu a ya\u0199in Rasha da Ukrane, yayin da ake tsare da \u00a02, a wani mataki da ake ala\u0199antashi da yaudarar matasan Afrika sama da dubu 1,780 da Rasha ta \u0257auka a \u0199asashe 36 .        <\/p>\n<p class=\"m-pub-dates\">Wallafawa ranar: 02\/03\/2026 &#8211; 09:08<\/p>\n<p>    Minti 1    Lokacin karatu\n<\/p>\n<p>Ministan har\u0199o\u0199in wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, da ke bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya na mai cewa, sun kad\u0257amar da wani shiri na da\u0199ile tsarin yaudarar \u01b4an \u0199asar domin samun ayyukan yi a \u0199asashen waje, ta hanyar rusa haramtattun tsare-tsaren \u0257aukar ma&rsquo;aikata da aka yi wa la\u0199abi da &lsquo;dark web&rsquo;.<\/p>\n<p>Babban jami\u2019in diflomasiyar na Ghana, ya ce, duk da kyakkywar ala\u0199ar tattalin arziki da ta diflomasiya da ke tsakanisu da Rasha, ba za su yi \u0199asa a gwiwa ba, wajen wayar da kan al\u2019ummarsu game da hanyoyin da ya kamata su bi wajen samun ayyukan yi a \u0199etare.<\/p>\n<p>Jami\u2019in ya kuma bada misalin yadda wasu \u01b4an Afrika Ta Kudu suka gamu da ajalinsu a ya\u0199in na Rasha da Ukrane kamar yadda ma\u2019aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta bada tabbacin dawowa da wasu gawarwakin wasu daga cikin su .<\/p>\n<p>Ka zalika, rahoton leken asirin Kenya, ya sanar da cewa\u00a0 \u01b4an \u0199asar sama da dubu guda aka \u0257auka aikin ya\u0199in amma kuma an sami nasarar ceto wasu 27 daga cikin su.<\/p>\n<p>Ablakwa, ya \u0199ara jaddada cewa, suna da labarin \u01b4an Ghanan kusan 300 da aka yaudaresu zuwa ya\u0199in cikin rashin sani, wanda kuma ba yakin su ba ne dan haka ba za\u2019a bar matasan \u0199asar kara zube ba, \u00a0za\u2019a ci gaba da wayar musu da kai.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"Gwamnatin Ghana ta ce, \u01b4an \u0199asar 55 ne suka mutu a ya\u0199in Rasha da Ukrane, yayin da ake&hellip;\n","protected":false},"author":2,"featured_media":30214,"comment_status":"","ping_status":"","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":"","_share_on_mastodon":"0"},"categories":[161],"tags":[5754,278,5779,233],"class_list":["post-30213","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","category-ghana","tag-afrika","tag-ghana","tag-rasha","tag-ukraine"],"share_on_mastodon":{"url":"https:\/\/pubeurope.com\/@afrique\/116159034343555554","error":""},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/30213","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=30213"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/30213\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/media\/30214"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=30213"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=30213"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/afrique\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=30213"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}