{"id":81695,"date":"2026-05-13T15:24:12","date_gmt":"2026-05-13T15:24:12","guid":{"rendered":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/81695\/"},"modified":"2026-05-13T15:24:12","modified_gmt":"2026-05-13T15:24:12","slug":"duniya-labari-mahajjaciya-daga-najeriya-ta-riga-mu-gidan-gaskiya-a-saudiyya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/81695\/","title":{"rendered":"Duniya Labari: Mahajjaciya daga Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Saudiyya"},"content":{"rendered":"<p>        An yi rashi na daya daga cikin Alhazan Najeriya da suka isa kasa mai tsarki watau Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2026Wata mahajjaciya da ta fito daga jihar Nasarawa ta yi bankwana da duniya tana da shekara 70 a birnin Makka na kasar SaudiyyaHukumar jin dadin Alhazai ta jihar Nasarawa ta bayyana cewa marigayiyar ta yi korafin rashin lafiya, sai dai duk da kokarin da likitoci suka yi, ba su samu damar ceto ranta ba<\/p>\n<p class=\"align-left\">\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200b\u200bEditan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al&#8217;amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi <\/p>\n<p class=\"align-left\">Birnin Makka, Saudiyya &#8211; Wata mahajjaciya &#8216;yar Najeriya daga jihar <a href=\"https:\/\/www.legit.ng\/tags\/nasarawa-state-news-today\/\" rel=\"noopener nofollow\" target=\"_blank\">Nasarawa<\/a>, Hajiya Rukayya Halliru, ta rasu a birni mai tsarki na Makka da ke kasar Saudiyya.<\/p>\n<p class=\"align-left\">Hukumar jin da\u0257in Alhazai ta jihar Nasarawa ta tabbatar da rasuwar marigayiyar a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/hausa.legit.ng\/kannywood\/1709855-ikuku-rahama-sadau-ta-yi-taaziyyar-da-rasuwar-jarumin-fim-a-najeriya\/\" class=\"c-article-read-also__image-wrapper\" rel=\"nofollow noopener\" target=\"_blank\"><img src=\"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/58d197cadc7fd0ff.jpeg\"   loading=\"lazy\" decoding=\"async\"\/><\/a><a href=\"https:\/\/hausa.legit.ng\/kannywood\/1709855-ikuku-rahama-sadau-ta-yi-taaziyyar-da-rasuwar-jarumin-fim-a-najeriya\/\" class=\"c-article-read-also__headline\" rel=\"nofollow noopener\" target=\"_blank\"><\/p>\n<p class=\"c-article-read-also__caption\">Kara karanta wannan<\/p>\n<p class=\"c-article-read-also__headline-wrapper\">Ikuku: Rahama Sadau ta yi ta&#8217;aziyyar rasuwar jarumin fim a Najeriya<\/p>\n<p><\/a><img class=\"article-image__picture\"  src=\"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/9fcd4c17c35cf6b6.jpeg\"  alt=\"Hajiya daga Najeriya ta rasu a Saudiyya\" title=\"Hajiya daga Najeriya ta rasu a Saudiyya\" width=\"1120\" height=\"630\" decoding=\"async\" fetchpriority=\"high\"\/>Maniyyata mata daga Najeriya na shiga jirgin sama<br \/>\nHoto: @hajjreporters<br \/>Source: Twitter<\/p>\n<p class=\"align-left\"><a href=\"https:\/\/dailytrust.com\/nigerian-pilgrim-dies-in-makkah\/\" target=\"_blank\" rel=\"nofollow noopener\">Jaridar Daily Trust <\/a>ta kawo rahoton cewa shugaban hukumar, Mallam Idris Ahmad Almakura, ya bayyana faruwar lamarin ga manema labarai a Makka.<\/p>\n<p>Mahajjaciya daga Nasarawa ta rasu a Makka<\/p>\n<p class=\"align-left\">Ya ce marigayiya Hajiya Rukayya Haliru, wadda ta fito daga \u0199aramar hukumar Keffi, tana da shekaru 70 a duniya.<\/p>\n<p class=\"align-left\">A cewar jami\u2019in, ta yi kukan rashin lafiya ne, kuma duk da \u0199o\u0199arin da likitoci suka yi, ta yi bankwana da duniya a safiyar yau.<\/p>\n<p class=\"align-left\">Shugaban hukumar tare da sauran jami\u2019ai da \u2019yan uwan marigayiyar, sun halarci asibitin domin kula da shirye-shirye da jigilar gawarta zuwa Masallacin Harami da ke Makka don gudanar da sallar jana\u2019iza.<\/p>\n<p>An ba mahajjata shawara kan kula da lafiya<\/p>\n<p class=\"align-left\">Ya kuma shawarci sauran Alhazai da su rika kula da lafiyarsu yadda ya kamata kuma su kai rahoton duk wata alama ta rashin lafiya cikin gaggawa ga likitocin da ke aiki tare da hukumar, jaridar Tribune ta kawo labarin.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/hausa.legit.ng\/news\/1709537-hajjin-bana-maniyyaciya-daga-taraba-ta-yi-bankwana-da-duniya-awanni-kadan-kafin-tafiya-saudiyya\/\" class=\"c-article-read-also__image-wrapper\" rel=\"nofollow noopener\" target=\"_blank\"><img src=\"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/1778685852_727_9fcd4c17c35cf6b6.jpeg\"   loading=\"lazy\" decoding=\"async\"\/><\/a><a href=\"https:\/\/hausa.legit.ng\/news\/1709537-hajjin-bana-maniyyaciya-daga-taraba-ta-yi-bankwana-da-duniya-awanni-kadan-kafin-tafiya-saudiyya\/\" class=\"c-article-read-also__headline\" rel=\"nofollow noopener\" target=\"_blank\"><\/p>\n<p class=\"c-article-read-also__caption\">Kara karanta wannan<\/p>\n<p class=\"c-article-read-also__headline-wrapper\">Hajjin bana: Maniyyaciya daga Taraba ta rasu awanni kadan kafin tafiya Saudiyya<\/p>\n<p><\/a><\/p>\n<p class=\"align-left\">Mallam Idris Ahmed Almakura ya mi\u0199a ta\u2019aziyyar hukumar ga gwamnatin jihar Nasarawa, iyalan marigayiya Hajiya Rukayya Halliru, da daukacin ma\u2019aikata da shugabannin hukumar jin da\u0257in Alhazai.<\/p>\n<p class=\"align-left\">A wata tattaunawa, Abdulwab Aboki, \u0257aya daga cikin dangin marigayiyar wanda ya shaida yadda aka gudanar da komai, ya nuna godiyar iyalinsu ga hukumar saboda goyon baya da gaskiyar da ta nuna a tsawon wannan mawuyacin lokaci.<\/p>\n<p><img class=\"article-image__picture\"  src=\"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/21970ecb96cddf32.jpeg\"  alt=\"'Yar Najeriya ta rasu a Saudiyya\" title=\"'Yar Najeriya ta rasu a Saudiyya\" width=\"1120\" height=\"840\" decoding=\"async\" loading=\"lazy\"\/>Mahajjatan Najeriya a kasa mai tsarki<br \/>\nHoto: @hajjreporters<br \/>Source: TwitterKaranta wasu labaran kan mahajjatan NajeriyaBarayi sun yi wa maniyyata sata a Saudiyya<\/p>\n<p class=\"align-left\">A <a href=\"https:\/\/hausa.legit.ng\/news\/1709728-majajjatan-jigawa-sun-gamu-da-matsala-a-saudiyya-barayi-sun-masu-tas-a-makkah\/\" target=\"_blank\" rel=\"nofollow noopener\">wani labarin<\/a> kuma, kun ji cewa wani mahajjaci dattijo Bafullatani wanda ya fito daga jihar <a href=\"https:\/\/www.legit.ng\/tags\/jigawa-state-news-today\/\" rel=\"noopener nofollow\" target=\"_blank\">Jigawa<\/a> ya bayyana cewa an yi masa fashin makudan kudi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.<\/p>\n<p class=\"align-left\">Dattijon mai suna Baba Katanga daga kauyen Katanga da ke karamar hukumar Kiyawa ya ce ya rasa dala 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel dinsa.<\/p>\n<p class=\"align-left\">Hakzalika, wani mahajjaci Bafullatani daga karamar hukumar Jahun shi ma ya rasa dukkan dalolinsa bayan da ake zargin wani direban tasi ya sace masa su.<\/p>\n<p>Asali: Legit.ng<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"An yi rashi na daya daga cikin Alhazan Najeriya da suka isa kasa mai tsarki watau Saudiyya domin&hellip;\n","protected":false},"author":2,"featured_media":81696,"comment_status":"","ping_status":"","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[91],"tags":[169,168],"class_list":{"0":"post-81695","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-riga","8":"tag-latvia","9":"tag-riga"},"share_on_mastodon":{"url":"https:\/\/pubeurope.com\/@dk\/116567963761035059","error":""},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/81695","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=81695"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/81695\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/media\/81696"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=81695"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=81695"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.europesays.com\/dk\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=81695"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}